APC ta sake dage ranar gudanar da zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa

Jam’iyar APC ta sake dage ranar da zata gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa daga ranar 25 ga watan Satumba ya zuwa ranar 27 ga Satumba.

Yekini Nabena mai rikon muƙamin kakakin jam’iyar shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Nabena ya kuma ce yan jam’iyar su tabbatar sun karbi katun shedar jam’iyarsu na din-din daga mazabunsu.

“Zaben fidda gwanin shugaban kasa na kai tsaye da aka shirya gudanarwa ranar Talata 25 ga watan Satumba,2018 yanzu zai gudana ranar Alhamis 27 ga watan Satumba, 2018,” sanarwar ta ce.

“Cikakkun yan jam’iyar masu rijista za su karbi katin kasancewarsu mamba na dindindin daga mazabunsu.”

Babu wani dalili da aka bayar na wannan canji da aka samu.

Shugaban kasa Muhammad Buhari shine ɗan takara daya tilo da ya tsaya a zaɓen.

More from this stream

Recomended