APC ta kuntata wa ‘ya’yanta — Gwamnan Nasarawa

Gwamnan jihar Nasarawa da ke Najeriya Umaru Tanko Almakura ya ce jam’iyyarsu ta APC ta kuntatawa wasu manyan ‘ya’yanta shi ya sa suka yi fushi da ita.

Gwamna Almakura na cikin ‘yan kwamitin da APC ta nada domin yin sulhu da ‘yan jam’iyyar da suka fusata da ita sakamakon rashin adalcin da suka ce an yi musu lokutan zabukan fitar da gwani.

A tattaunawarsa da BBC, gwamnan na jihar Nasarawa ya ce za su yi bakin kokarinsu wurin ganin sun rarrashi ‘yan jam’iyyar da aka batawa rai.

“Wadansu ba kudin da suka kashe ne ya bata musu rai ba. Wadansu mutuncinsu, girmansu, martabarsu da kuma wahalar da suka dauka suka yi da wannan jam’iyya na tsawon lokaci…su zo a lokaci daya a kuntata musu. Wannan yana kawo bacin rai.”

Gwamnan ya ce illar da hakan zai yi ga jam’iyyar tana da yawa, yana mai cewa “domin mafi yawan mutanen da suka zamo ‘yan takara su ne alkiblar jam’iyyar.”

Sai dai ya ce duk da haka za su je su saurari wadannan ‘yan jam’iyya da zummar dinke barakar da kuntata musu ka iya haifarwa a zaben 2019.

More from this stream

Recomended