Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kafa kwamitin da zai saurari korafe-korafen ‘yan jam’iyyar kan yadda zaben fitar da gwani ya gudana a fadin kasar.
Shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshimole ne ya kafa kwamitin ranar Litinin, bayan kammala zabukan fitar da gwanin, wandanda suke cike da korafe-korafe a jihohi da dama.
Kwamitin yana karkashin tsohon gwamnan jihar Edo Farfesa Oserheimen Osunbor.
Wakilan kwamitin sun hada da Alh. Musa Gwadabe, da Bashorun Reuben Famnyibo da Alhaji Abdulrahman Adamu, sai kuma Mike Ugwa a matsayin sakatare.
‘Yan jam’iyyar a jihohin kasar da dama sun yi zargin danniya da rashin adalci da murdiya a zabukan da aka gudanar, musamman a kujerun gwamna da na ‘yan majalisa.
Ko mai dakin Shugaban kasar Aisha Buhari ta koka kan abinda ta kira rashin adalcin da jam’iyyar ta yi wa wasu ‘yan takara.
Wasu kuma da suka tsaya takarar sun yi zargin cewa sun ci zaben, amma ana murde musu aka bayyana sunayen wasu daban.
Korafin wasu ‘yan APC din kuma shi ne rashin gudanar da zaben, amma kuma aka bayyana sunayen wasu a matsayin wadanda suka yi nasara.
Wasu dai na ganin matukar jam’iyyar ba ta warware wadannan matsaloli ba, to za ta shiga manyan zabukan kasar da matsalolin cikin gida da kuma na jam’iyyun hamayya, musamman ma PDP.
Abinda ‘yan jam’iyyar ta APC da ma ‘yan Najeriya za su zuba ido su gani shi ne, ko kwamitin zai iya warware matsalolin da suka biyo bayan zabukan na fitar da gwani gabanin cikar da wa’adin da hukumar zaben kasar INEC ta dibar wa jam’iyyun.