Ana zargin dogarin Aisha Buhari da karbar biliyoyin Naira

Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari

Ana zargin babban dogarin uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari, da laifin karbar kudade daga wasu fitattun mutane a kasar da sunanta.

Uwargidan Shugaban Najeriya Aishatu Buhari ta tabbatar da cewa babban dogarin na hannun jam’ian tsaron kasar inda yake fuskantar bincike.

Ana dai zargin CSP Sani Baban Inna da kakkarbo kudaden da yawansu ya kai Naira biliyan biyu da rabi daga wasu jami’an gwamnati da abokan arzikin uwar dakinsa da sunan tallafi zuwa gareta.

Sai dai dangin jami’in ‘yansandan sun musanta wannan zargin.

Tun a ranar jumu’ar da ta gabata ne dai bayanai suka ce aka kama dogarin na uwar gidan Shugaban kasa Aishatu Buhari a yayin wani samame da ‘yan sanda suka kai gidansa bayan da tayi zargin cewa ya zambace ta zunzurutun kudi har Naira miliyan dubu biyu da miliyan dari biyar.

Sai dai kuma in ji bayanan binciken da aka yi a gidan nasa da kuma a asususn ajiyarsa na banki ya nuna babu alamun makudan kudi irin haka a cikinsu.

Amma kuma sakamakon binciken bai kwantawa uwar dakin tasa rai ba ganin cewa ‘yan uwansa ‘yan sanda suka yi binciken.

Uwargidan shugaban kasa Buhari ta mika maganar ga hannun hukumar ‘yan sandan ciki wato SSS wadda ke ci gaba da binciken wannan maganar kawo yanzu.

Sai dai kuma wata sanar wa da ofishinta ya fitar, Hajiya Aisha Buhari ta ce ba ta da hannu a kama shi da kuma tsarewar da aka ci gaba da yi masa.

Sulaiman Haruna shi ne mai magana da yawunta:

“Kamar yadda kowa ya sani, jami’in ‘yan sanda ne, kuma hukumar ‘yan sanda ce da kanta ta kama shi domin ta bincike shi akan wasu zarge-zarge da aka yi masa cewa yaje ya karbi kudade da sunanta, da sunan ‘ya’yanta cewa suna neman kudi.”

Ya kara da cewa, “Kuma an sami labarin cewa ya karbi kudade da yawa a hannun mutane.”

Ko dai mene ne CSP Sani Baban-inna na tsare a halin yanzu yana fuskantar bincike kan wannan zargin da uwargidan shugaban kasar ke yi masa.

Yayin da a bangare guda iyalinsa suka tsaya kai da fata cewa dan uwansu bai aikata laifi makamancin wannan ba.

Ga ta bakin yayansa Faruk Baban-Inna:

“Dan uwanmu mai gaskiya ne, bai aikata wannan laifin ba, mu a matsayin ‘yan uwansa mun tabbatar da haka.”

Ga alamu ‘yan kasar ba su da damuwa ga kamawa da kuma binciken ake yi wa jami’in dan sandan; wasu na da damuwar ne kan yadda ake ci gaba da tsare shi fiye da sa’oi 24 ba tare da gurfanar da shi gaban kotu ba.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake kama wani a kasar bisa zargin karbar kudade daga jama’a da sunan uwargidan shugaban kasar ba.

Ko a watan Janairun bana ma, ‘yan sanda a Abuja babban birnin Najeriya sun gurfanar da wata mata mai shekara 37 a gaban kotu bisa zarginta da neman kwangiloli da karbar kudade daga jama’a da suna cewa ita ce Aisha Buhari.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...