Ana zanga-zangar nuna damuwa da yawaitar kashe-kashe a Zamfara

Zanga zanga a Zamfara

Al’ummar jihar Zamfara a arewacin Najeriya na gudanar da zanga-zanga domin nuna damuwa da yawaitar kisan rayuka da ake yi a sassan jihar.

Ana gudanar da zanga-zangar ne a karamar hukumar mulki ta Tsafe, da ke nisan kusan kilomita 50 da Gusau babban birnin jihar.

Rahotanni sun ce matasa da ‘yan gudun hijira da suka kunshi mata da yara kana sun toshe babbar hanyar da ke zuwa Gusau, tare da kone wasu gine-ginen gwamnati.

Rundunar ‘yan sandan jihar da ta tabbatar da faruwar al’amarin ta ce ta kama wasu daga cikin masu zanga-zangar kamar yadda kakakin ‘yan sandan DSP Muhammad Shehu ya shaida wa BBC.

Mazauna garin na tsafe na bayyana damuwa ne kan yadda masu gudun hijira ke ci gaba da tururuwa a yankin, suna guduwa sakamakon hare-haren da ake zargi yan bindiga da barayin shanu ke kai wa.

Masu zanga-zangar sun bayyana cewa, sun gaji da halin ko-in-kula da hukumomi suke nunawa a kan rashin tsaro a jihar.

Shugaban karamar hukumar Tsafe Alhaji Abubakar Aliyu ya shaida wa BBC cewa, sama da mutum 40 ne suka rasa rayukansu a kauyuka daban-daban cikin mako biyu.

A makon da ya gabata ne, aka kashe mutane da dama a wani hari da aka kai a kauyen Birnin Magaji, inda nan ne kauyen da minstan tsaro a Najeriya ya fito.

    Gwamnatocin da suka mulki kasar a jejjere sun ta yin buris wajen kawo maslaha ta dindindin kan matsolin da ke addabar jihar.

    A yayin da matsalar barayin shanu ta zama bala’i ga jihar Zamfara, Gwamna Abdulaziz Yari ya samar da kungiyar ‘yan kato da gora don yakar maharan a shekarar 2013.

    Sai dai ba a dauki dogon lokaci ba mazauna yankin suka fara korafi kan ‘yan kato da gorar, wadanda a yanzu su ma suke gallabar mutanen da ya kamata su kare da sace-sace.

    Hakan ta sa kauyukan da ke fama da matsalar barayin shanu da ‘yan kato da gora suka fara kokarin ganin sunkare kansu da duk abun da ya kamata.

    Daga haka sai rikicin ya kara ruruwa ta hanyar kai hare-hare da daukar fansa. A haka sai a ka kasa cimma kokarin shirin yin afuwa da aka so gabatarwa.

    Zamfara ta fara kaddamar da shari’a a Najeriya

    A yanzu dai ana ganin yadda rikici ke kara bazuwa da karuwa kuma ga alama ba a san hanyoyin da za a bi a shawo kansa ba.

    Abun da yake a bayyane kawai shi ne yadda dumbin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ke ci gaba da mutuwa.

    Gwamman mutane sun mutu a ‘yan watannin da suka gabata sakamakon hare-haren da aka kai wasu kauyuka a jihar Zamfara.

    Sai dai saboda rashin isassun maso kawo bayanai, zai yi wahala a fadi adadin mutanen da suka mutu a rikicin da aka shafe shekara shida ana yi.

    A tsawon shekarun da suka gabata ana ci gaba da samun matsalolin satar mutane don kudin fansa da kuma fyade a wasu kauyuka na jihar Zamfara.

    More from this stream

    Recomended