“Ana buƙatar wanda ba ɗan amshin shata ba ya shugabancin EFCC”

Shugaba Buhari

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Wasu ‘yan fafutuka a Najeriya sun ce jagorancin hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa na buƙatar wani ƙwaƙƙwaran jigo da zai yi aiki da gaske, kuma ba za a yi amfani da shi wajen cin mutuncin ‘yan adawa ba.

Suka ce shugaban hukumar na gaba sai kuma ya kasance wanda ba zai bar wasu shafaffu da mai ba saboda kusancinsu da gwamnati mai ci ko shugaban ƙasa.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da bayanai ke cewa Shugaba Muhammadu Buhari na laluben mutumin da zai nada a matsayin sabon shugaban hukumar EFCC, bayan dakatar da Ibrahim Magu.

Kwamared Auwal Musa Rafsanjani, babban jami’in kungiyar Transparency International a Najeriya, ya ce daya daga cikin manyan ƙalubalan da magajin Magu zai fuskanta shi ne farfado da martabar hukumar da wasu ke ganin ta zube a yanzu.

A ranar Talata ne gwamnati ta dakatar da Ibrahim Magu bayan wani kwamiti ya fara bincike a kan zargin nuƙu-nuƙu wajen bayyana kuɗaɗe da kadarorin da hukumar ta kwato daga hannun wasu jami`an gwamnati.

Masu fafutuka irinsu Rafsanjani na ganin cewa akwai ɗumbin ƙalubale a gaban duk wanda za a dauko don ya shugabanci hukumar bisa la’akari da abubuwan da suka faru.

‘Bisa al`ada `yan sandan ne ake nadawa su shugabanci EFCC, amma ‘yan fafutukar yaki da rashawa na ganin cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta sake salo wajen zaɓar wanda zai shugabanci hukumar.

Hakkin mallakar hoto
Kabiru Dakata Facebook

Image caption

Kabiru Dakata, shugaban kungiyar CAJA, mai rajin tabbatar da shugabanci na gari a Najeriya

Kwamared Kabiru Dakata,na kungiyar CAJA, mai rajin tabbatar da shugabanci na gari, ya ce kamata ya yi gwamnati ta yi wa dokokin EFCC gyaran fuska, ta yadda za a samu damar sauya salo, maimakon takaita mukamin ga `yan sanda.

”Tun da bangaren yan sanda sun yi har sau hudu an ga inda suka yi nasara, an ga inda suka gaza to kamata ya yi a jarraba wasu masu damarar, wadanda suke ci ko wadanda suka yi ritaya”.

Ya jaddada bukatar yin duban tsanaki kan duk wanda za a dauko don ba shi shugabancin hukumar EFCC, jagorar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya.

A cewarsa, matuƙar aka lura akwai matsala a lokacin da ya kwashe yana aiki, to kuwa bai cancanci a ba shi jagorancin hukumar ba.

More News

Ƴan bindiga sun ƙone ginin hedkwatar ƙaramar hukuma tare da kashe jami’an tsaro

Ƴan bindiga sun kai farmaki hedkwatar ƙaramar hukumar, Isiala Mbano dake jihar Imo da tsakar daren ranar 3 ga watan Satumba inda suka ƙone...

An kama wasu ƴanta’adda da ke da alaƙa da Turji

Akalla mayaka 18 da ke da alaka da fitaccen shugaban ‘yan ta’adda Bello Turji aka kama a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin...

Dakarun Najeriya sun kai farmaki wa ƴan’adda a Borno, wani kwamanda ya miƙa wuya

Rundunar sojin Najeriya ta sanar a ranar Lahadin cewa dakarunta sun yi nasarar kashe wani fitaccen kwamandan kungiyar Boko Haram, Abu Rijab da wasu...

Yadda wani adalin direba ya kawo cigiyar haka maƙare a kuɗi

Wani direban motar kasuwa ya mayarwa rundunar ‘yan sandan jihar Kano jakar da ta bata dauke da makudan kudade.  Direban mai suna Safiyanu Mohammed...