
A ranar Juma’a ne rundunar Sojan Najeriya ta binne gawarwakin sojojin da aka kashe a harin da yan ta’addar kungiyar Boko Haram suka kai kan sansanin sojoji dake Metele a karamar hukumar Guzamala ta jihar Borno.
Ya yin da akawai rahotannin dake cewa sojoji sama da 100 aka kashe rundunar sojan ta ce jami’anta 23 ka wai aka kashe a harin na Metele wanda aka kai wa dakarun ranar 18 ga watan Nuwamba.
An binne sojojin ne a makabartar sojoji dake barikin sojoji na Maimalari a Maiduguri.
Bikin jana’izar wanda malaman addinin musulunci dana kirista suka jagoranta ya samu halartar manyan jami’an sojoji, jami’an gwamnati,wakilan shehun Borno da kuma iyalan mamatan.
Tukur Buratai, babban hafsan sojijin kasa na Najeriya ya bayyana harin da ya faru a matsayin wani abu mummuna inda yace sojojin sun sadaukar da kansu wajen kare kasa da kuma tabbatar da kasarnan ta cigaba da zama dunkulalliya.