An yi garkuwa da mutane da dama a Zamfara

[ad_1]

Zamfara

Hakkin mallakar hoto
ABDULRAZAK BELLO KAURA

Wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun sace mutane da dama a kan wata babbar hanya da ta hada jihar Zamfara da makwabciyarta Katsina, kamar yadda rahotanni daga jihar suka bayyana.

Bayanai sun ce mutanen da aka sace suna komawa gida ne bayan kammala bukukuwan babbar sallah, a wannan makon.

Wani mazaunin daya daga kauyukan da ke kan hanyar ya shida wa BBC cewa ya ga ‘yan sanda sun dauko motar fasinja, wadda ba kowa a cikinta, wanda ya ce “masu garkuwar ne suka kwashe mutanen da ke cikinta.”

Haka kuma wani mazaunin yankin ya ce ‘yan sanda sun kuma kwaso wasu babura da ake kyautata zaton cewa suma an yi garkuwa da masu su ne.

Mataimakin daraktan watsa labarai na rudunar sojan da ke jihar Kanal Muhammad Dole ya tabbatarwa BBC faruwar lamarin.

Ya ce masu satar mutane sun farwa hanyar ne saboda yadda ake fatattakar su daga garuruwan da suka addaba a baya.

Sai dai ya ce jami’an tsaro suna kokarin “farautar masu aikata laifukan, duk inda suka shiga.”

Dakarun tsaron kasar da suka hada da sojojin sama da na kasa, da jami’an ‘yan sanda dai sun kaddamar da wani gagarumin aiki na farautar masu sata da garkuw da mutane da suka addabi jihar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya tura dakarun sakamakon yawon korafe-korafe da aka yi kan aikin masu garkuwa da mutane “da suke cin karensu ba babbaka” a jihar ta arewa maso yammacin kasar.

Kawo yanzu dai babu bayani daga hukumomi kan adadin mutanen da aka yi garkuwar da su a kan hanyar da ake bi ta Mafara.

Lamarin dai yana faru ne tsakanin kauyen Koloni zuwa Goran Na Mahe zuwa Kaya zuwa Faru.

Hanyar dai wani yanke ne ga masu zirga-zirga tsakanin Katsina da jihohin Sakkwato da kuma Zamfara.

A cewar wani mazaunin daya daga kauyukan da ke yankin ‘yan fashsin sun mayar da hanyar tamkar hanyar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Mutumin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce masu satar mutanen suna yawan fitowa su tare hanya su kuma shige daji da mutanen da suke tafiya a motoci ko a babura.

Ya ce idan ka gansu za ka ce ma’aikata ne. “Suna sa kakin soji, ko na jami’an kare hadura, ko na jami’an hana fasa kwauri a lokacin da suke tare hanya.” in ji mutumin.

Rahotanni sun ce matafiya suna son bin hanyar, saboda kyawunta.

[ad_2]

More News

Atiku ya bayar da tallafin miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri babban birnin...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

Mutanen Sokoto na ta murnar kashe ƙasurgumin ɗanbindigar nan Halilu Buzu

Mazauna yankin Sokoto da kewaye na murnar kashe wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Kachallah Halilu Buzu, da sojojin Najeriya suka yi a farmakin da...