Alkali Yusuf Halilu, shi ne ya yanke hukuncin na kisa akan Maryam bayan an kwashe lokaci mai tsawo ana sauraren jawaban lauyoyi masu kare ta, da wadanda ke tuhumar ta da laifin kashe mijinta.
Yanke hukuncin ke da wuya, sai Maryam Sanda ta dinga kwarma ihu ta na cewa “Innalillahi Wa Innailaihir Rajiun” kuma sai ta soma gudu daga wurin bada shaida inda take tsaye bayan da aka karanta hukuncin, har ta kawo rudani a cikin kotun.
Wannan shari’a ta dauki lokaci mai tsawo domin an ba da belin Maryam Sanda a shekarar 2018 saboda ta na dauke da juna biyu a lokacin da al’amarin ya auku kuma ta yi ta fama da rashin lafiya.
Duk da cewa wannan hukunci ne mai zafi, an ba Maryam Sanda dama ta daukaka kara.
Bayan yanke wanan hukuncin ma’aikatan kotun sun tusa keyar Maryam zuwa gidan kurkuku da ke garin Suleja inda za ta yi zaman jira har sai ta daukaka kara.
To sai dai Lauyan da ya kare marigayi Bilyaminu, Barista Fidelis Ugogbe ya ce su na yi wa Allah godiya da ya sa yau iyalan marigayin, hankalin su zai kwanta domin sun sami hukunci daidai da burin su, kuma wanan ya nuna cewa lallai kotu ita ce wurin da kowa ke iya kai kukan sa a share masa hawaye.
“Yau an share wa dangin Bilyaminu hawaye.” inji Baristan ya kuma ce, ko da yake an ba Maryam dama ta daukaka kara amma su na jira, a duk lokacin da aka neme su, za su bada ba’asi kamar yadda suka saba saboda a tabbatar da wanan hukunci.