An tsagaita buda wuta a Yemen

'Yan tawayen Huthi a Yemen

‘Yan tawayen Houthi a Yemen sun ce za su dakatar da hare-haren makamai ma zu linzame da suke kai wa kan kawancen da saudiyya ke jagoranta, domin mutunta kiran Majalisar Dinkin Duniya na kokarinta na kawo karshen yaki a Yemen.

Sanarwar na zuwa ne bayan kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya bada umarnin dakatar da bude wuta a garin Hodeida da ke gabar teku.

‘Yan tawayen na Huthi a Yemen sun ce a shirye suke su dakatar da bude wuta idan har bangaren da ke yaki da su na kawancen da Saudiyya ya tsagaita bude wuta.

Karuwan matsin lambar kasashen duniya kan bangarorin biyu na kawo karshen yakin da ya kashe mutum sama da dubu 10 ya jefa kasar Yemen cikin matsanancin hali na yunwa.

Tsagaita buda wutar kuma na zuwa ne karkashin kokarin Majalisar Dinkin Duniya na farfado da tattaunawar sulhun da aka kasa yin nasara a tsawon shekaru uku da aka kwashe ana yaki.

Kasashen yammaci da ke taimakawa kawancen na Saudiya da makamai, yanzu sun fara nuna damuwa a rikicin musamman tun bayan kisan dan jaridar kasar Saudiyya mazaunin Amurka Jamal Kashoggi da aka kashe a wani karamin ofishin jekadancinta a Turkiya.

A yau ne ake sa ran Birtaniya za ta gabatar da wani daftarin gaban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan dakatar da bude wuta da yadda za a samu kai kayan agaji ga mutanen kasar.

More from this stream

Recomended