
A yau Talata, Gwana Nasir El-Rufai ya jagoranci taron majalisar tsaro ta jihar
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Twitter, sai dai ba duka sassan jihar ba ne aka sassauta dokar.
An sassauta dokar a birnin Kaduna, inda a yanzu dokar za ta fara aiki daga karfe 5 na yamma zuwa karfe 1 na rana.
Wannnan na nufin kenan mutane za su iya zirga-zirgansu da harkokinsu a birnin tsakanin karfe 1 na rana zuwa karfe 5 na yamma.
Har ila yau, gwamnan ya ce akwai unguwannin da dokar hana fita za ta cigaba da aiki wadanda su ne Kabala West da Kabala Doki da Narayi da Maraban Rido.