Hukumomi sun sanar da ganin jinjirin watan Ramadan a Saudiyya a ranar Juma’a, lamarin da ya tabbatar da cewa azumin watan Ramadan zai fara a ranar Asabar, 1 ga Maris, 2025.
In ba a manta ba, Sultan na Sokoto kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bukaci al’ummar Musulmi da su ma su duba watan Ramadan 1446 AH tun a ranar Alhamis.
Sai dai har yanzu bai bayar da karin bayani ba kan ko an ga watan a Najeriya.
A halin da ake ciki, kasashe kamar Qatar da Oman sun tabbatar da cewa za su fara azumi a ranar Asabar, 1 ga Maris.
Za a ci gaba da dakon sanarwar hukuma daga Najeriya dangane da ganin watan Ramadan.