An gano gawarwakin ƴan gudun hijira 28 kusa da wata cibiyar tsare masu ƙoƙarin ketare iyaka a hamadar kudancin Libya.
A cikin wata sanarwa da Ofishin Babban Lauyan Gwamnatin Libya ya fitar a ranar Lahadi, an bayyana cewa an gano ramin a birnin Kufra, inda aka tsare ɗaruruwan ƴan gudun hijira.
Jami’an tsaro sun ceto mutane 76 daga wannan wurin tsarewar.
Rahotanni sun nuna cewa wata ƙungiyar masu aikata laifi ta tauye wa waɗannan ƴan gudun hijira ‘yanci, ta yi musu azaba, tare da ba su azabar da ta sabawa ɗabi’a da mutuncin ɗan adam.
Kufra na kudu maso gabashin Libya ne, a yankin hamada da ke kusa da iyakokin ƙasashen Masar da Sudan.
Tsaro a Libya na ci gaba da kasancewa cikin hatsari sakamakon shekaru da dama na yaƙin basasa.
Ƙungiyoyin ‘yan bindiga, wasu daga cikinsu na aiki tare da hukumomin gwamnati, na tafiyar da ƙungiyoyin fataucin mutane, inda ake cin zarafin ƴan gudun hijira, ‘yan gudun neman mafaka da kuma bakin haure.
Ana ci gaba da samun rahotanni kan take hakkokin bil’adama da suka haɗa da kashe mutane ba bisa ka’ida ba, tilasta shiga ƙungiyoyin ‘yan bindiga, tilasta aiki da kuma fataucin mata don amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba.
An Samu Gawarwakin Ƴan Gudun Hijira 28 A Rami Ɗaya A Libya
