An kashe fiye da mutane 100 a Jihar Filato

Rahotanni da suke fitowa daga Jihar Filato na nuna cewa an kashe mutane sama da 100.

Gwamna Mutfwang ya ce hare-haren ba su da tushe balle makama kuma an dora wa jami’an tsaro aikin bankado masu daukar nauyin wannan aika-aika.

Ya bayyana yadda wasu ‘yan ta’adda suka kai farmaki kan al’ummomi sama da 15 a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar a jajibirin Kirsimeti.

Maharan sun kona gidaje da dama a daren Lahadi.

More from this stream

Recomended