An kama yan shi’a 400 a Abuja

Ƴansanda sun kama yan kungiyar Yan Uwa Musulmi ta Najeriya su 400 lokacin zanga-zangar da suka gudanar ranar Talata a birnin tarayya Abuja.

Kwamishinan ƴansandan birnin tarayya Abuja, Bala Chiroma ya ce an samu bom 33 da ake haɗawa na cikin kwalba a hannun yan kungiyar a arangamar da aka yi a yankin Wuse dake birnin.

Ya’yan kungiyar ta shi’a sun yi arangamar ne da jami’an ƴansanda lokacin da suke gudanar da zanga-zangar neman a saki jagoran su Sheikh Ibrahim Elzakzaky.

An kona wata motar sintirin ƴansanda lokacin da rikici ya barke wannan ce dai motar jami’an tsaro ta uku da aka kona a birnin cikin sa’o’i 72.

Da yake wa manema labarai jawabi kwamishinan ya ce biyu daga cikin masu zanga-zangar an kama su ne lokacin da suke kokarin shigowa da bom din fetur cikin birnin.

Ya bayyana wadanda aka kama da suna Mustafa Abdullahi da aka kama da kwalbar bam 18 da kuma da kuma Abdullahi Umar da aka kama da jaka mai dauke da irin wancan bom 13.

More from this stream

Recomended