Rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun ta kama wani manomi mai shekaru 53 mai suna Oloyede David bisa zargin satar buhuna uku na abarba da darajarsu ta kai N90,000 a yankin Orile-Ilugun da ke karamar hukumar Odeda.
Rahotanni sun bayyana cewa an kama David ne yana girbin abarbun daga gonar wata mata mai suna Ola Omotayo.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Omolola Odutola, ta tabbatar da kamen, inda ta ce an cafke wanda ake zargin ne da misalin karfe 11:58 na safe a ranar Talata.
Ta ce wani manomi ne ya hango shi yana kwasar abarbun, inda ya gaggauta sanar da sauran manoma, wadanda suka hadu suka cafke shi.
“A lokacin da aka kama David, yana dauke da buhuna uku na abarba da kimanin darajarsu ta kai N90,000. Daga nan aka kira mai gonar, wadda ta tabbatar da cewa an sace mata abarbun,” in ji Odutola.
Bugu da kari, Omotayo ta ce an taba sace mata abarbun da darajarsu ta kai N650,000 da kuma injin ban ruwa mai darajar N180,000 daga gonarta a baya.
Tuni dai aka mika wanda ake zargin da abarbun da aka kwato zuwa ofishin ‘yan sanda, inda aka tura karar zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar.
An Kama Wani Mutum Bisa Laifin Satar Abarba a Ogun
