
Rundunar sojan Najeriya shiya ta daya dake Kaduna ta kama wani mai safarar bindigogi akan hanyar Borgu dake karamar hukumar New Bussa ta jihar Niger.
Mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar sojan,Kanal Muhammad Dole shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.
Dole, ya ce atisayen da rundunar take gudanarwa da aka yi wa lakabi da Operation Whirl Punch a dukkanin jihohin da ake gudanar da shi a karkashin shiyar na cigaba da samun nasara.
Mutumin da aka kama mai suna, Rabi’u Akilu ya fito ne daga kauyen Dangulbi dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara kuma ya shiga hannu ne a wurin binciken ababen hawa na sojoji dake Goroji.
Akilu na dauke da bindigogi kirar gida manya da kanana da yawansu ya kai 46 da kuma kwanson harsashi 343.
Sanarwar ta kara da cewa har ila yau an same shi da wata mota kirar Toyota Corolla kuma yana cigaba da bada hadin kai a binciken da rundunar take.
Jihar Zamfara ta dade tana fuskantar hare-hare daga wasu gungun barayi.