Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta kama wani mutum mai suna Anas Yakubu, mai shekaru 33, bisa zargin kashe matarsa ta ‘yar uwa, Fatima Adamu, a kauyen Baura da ke Karamar Hukumar Albasu.
Wani mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama, ne ya bayyana kamun a shafinsa na X a ranar Litinin.
Rahotanni sun nuna cewa rikici ne ya barke tsakanin wanda ake zargi da mamaciyar a ranar 16 ga watan Maris da misalin karfe 12:30 na rana.
“Yakubu ya bugi Fatima Adamu, mai shekaru 35, da turmi a kanta, wanda hakan ya haddasa mata munanan raunuka,” a cewar rahoton.
Bayan faruwar lamarin, an garzaya da ita zuwa Asibitin Karamar Hukumar Albasu, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarta.
‘Yan sanda sun tabbatar da kama wanda ake zargi, yayin da aka mika gawar mamaciyar ga iyalanta domin gudanar da jana’iza bisa koyarwar addinin Musulunci.
An Kama Mutumin Da Ake Zargi Da Hallaka Ƴar’uwar Matarsa
