An Kama Mutane 12 Bisa Zargin Kashe Matashi a Masallaci a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Jihar Kaduna ta kama mutum 12 da ake zargi da kai hari kan wani masallaci a Kaduna, arewacin ƙasar.

Kakakin rundunar, DSP Mansur Hassan, ya bayyana a wata sanarwa cewa harin ya yi sanadin mutuwar wani matashi mai suna Usman Mohammad, mai shekara 23.

A cewarsa, rundunar ta samu rahoto daga wani mazaunin Rigasa cewa wasu ‘yan daba dauke da makamai na shirin kai hari kan masu sallar Tahajjud.

“Da samun rahoton, jami’ai suka bazama domin dakile harin, amma kafin su isa wurin, ‘yan daba sun riga sun daba wa Usman Mohammad wuka. Likita ya tabbatar da mutuwarsa a asibiti,” in ji DSP Mansur.

Ya ce an je wurin tare da dakarun sa-kai na Civilian Joint Task Force (CJTF), kuma bincike na ci gaba da gudana kan lamarin.

More from this stream

Recomended