An kai hari garin Katarko na jihar Yobe

Sojin Nigeria

Dakarun sojin Najeriya na ikirarin yin galaba kan ‘yan Boko Haram, amma an ci gaba da kai hare-hare a wasu yankunan kasar musamman arewa maso gabas

To rahotanni daga jihar Yobe a Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a garin Katarko da ke kusa da garin Damaturu.

Maharan sun abka garin ne da yammcin jiya laraba, inda suka bude wuta, lamarin da ya sa mutanen garin suka shiga daji.

Wani mutum da ya tsere daji tare da iyalansa, ya shaidawa BBC cewa tun da misalin karfe 5 na yammacin jiya maharan suka fara harbin kan mai tsautsayi dlilin da suka gudu kenan.

Ya kara da cewa hatta jami’n tsaro suma ba a bar su a baya ba dan tare suke dajin, mata da kananan yara sun firgita matuka inda suke cikin tashin hankalin rashin sanin abind ke faruwa ga ‘yan uwa da ke cikin garin.

kawo yanzu ba san ko akwai wadanda suka rasa rayukansu ko jikkat ba, ba wannan ne karon farko da mayakan da ake zaton ‘yan Boko Haram ne suka kai hari garuruwa da kuyukan jihar Yobe ba.

More from this stream

Recomended