A jiya Lahadi ne wasu magoya bayan gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, suka yi dandazo a harabar wasanni ta Lekan Salami dake birnin Ibadan a jihar Oyo domin gudanar da addu’o’i tare da gudanar da zanga-zangar lumana domin mika musu bukatunsu na ganin Abba Kabir ya cigaba da zama gwamnan jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta yanke, wadda ta soke nasarar Yusuf tare da bayyana dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.
A makon da ya gabata ne zanga-zangar ta barke a Kano sakamakon samun sabani a cikin kwafin ainihi na hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na korar Yusuf.