An yi garkuwa da wasu mutum 11 ƴan gida ɗaya

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ‘yan gida daya mutum 11 da suka hada da mata da ‘ya’yan wani dan jarida mazaunin Kogi, Muhammed Bashir, a jihar Kaduna.

Matar Bashir, Aminat, da ‘ya’yansa mata guda biyu, Aisha da Hajara, an ce sun isa Kaduna ranar Alhamis domin hutu tare da ‘yan uwanta.

Bashir, wakilin jaridar New Telegraph, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyanawa abokan aikinsa garkuwar ranar Juma’a a Lokoja. 

“Yan uwana, don Allah ina bukatar addu’arku, ‘ya’yana mata biyu da mahaifiyarsu, ciki har da wasu guda takwas, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne sun yi garkuwa da su jiya a Kaduna, inda suka je hutu.  Don Allah a yi mini addu’a,” kamar yadda ya rubuta a dandalin WhatsApp Chapel na Kogi.

Sauran ‘yan uwa a cewarsa sun hada da Aisha Saba Khadija, Haruna, Adamu Haruna, Muhammad Abubakar, Asmau Abubakar, Usman Abubakar, Muhammad Abubakar, da Hauwa Muhammad.

Ya ce ya tuntubi ‘yan sanda da ma’aikatar tsaron kasar kuma an ba su tabbacin cewa ana daukar matakan kubutar da wadanda lamarin ya shafa tare da kamo masu garkuwa da mutanen.

More from this stream

Recomended