Jami’an tsaro sun samu nasarar gano gawar, Manjo Janar Idris Alkali mai ritaya wanda aka bayyana bacewar sa ranar 3 ga watan Satumba.
An gano gawar tasa a wata rijiya da aka daina amfani da ita a yankin Guchwet, Shen a karamar hukumar Jos ta kudu.
Umar Muhammad, jami’in sojan da ya jagoranci aikin gano mamacin ya ce za ayi masa jana’iza ta girmama wa kafin daga bisani a binne shi.
Tun da farko dai sojoji sun samu nasarar gano wani kabari da aka binne gawar Janar din kafin daga bisani a tone shi daga nan.
Daya daga cikin mutanen da ake nema ruwa a jallo game da kisan wanda daga bisani ya mika kansa ga jami’an tsaro shine ya nuna inda rijiyar da aka jefa gawar take.