Amurka za ta daina tallafawa hukumar da ke tallafawa ‘yan gudun hijarar Falasdinu

[ad_1]

Hukumar na samar da abubuwan more rayuwa kamar makarantu da cibiyoyin lafiya

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Hukumar na samar da abubuwan more rayuwa kamar makarantu da cibiyoyin lafiya

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da cewa Amurkar za ta daina bayar da duk wani tallafin kudi ga Hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya mai tallafawa ‘yan gudun hijirar Falasdinu.

Ta kuma ce hukumar ta UNRWA na da rauni wanda ba zai iya gyaruwa ba.

Wani mai magana da yawun Hukumar ta UNRWA, Chris Gunness ya kare hukumar a jerin sakonni da ya wallafa a twitter. Ya ce “Ba za mu amince da sukar da a ke yi wa hukumar na cewa makarantunta da cibiyoyin lafiyarta da tsare-tsarenta na agajin gaggawa na da raunin da ba za a iya gyarawa ba.”

Wani mai magana da yawun Shugaba Mahmoud Abbas ya ce matakin da Amurkar ta dauka wani salo ne na horo, kuma zalunci ne ga al’ummarsa.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga sauran kasashen duniya da su cike gibin dala miliyan dari uku da hukumar bayar da agajin ta ke da shi.

Dangantaka tsakanin Amurka da Shugabannin Falasdinu ta tabarbare a ‘yan watannin nan, musamman ma tun da Shugaba Donald Trump ya yanke shawarar mayar da ofishin jakadancin Amurka birnin Kudus.

A watan Janairu ne dai Shugaban Amurkar Donald Trump ya bayyana cewa zai kawo wasu sauye-sauye saboda yankin na Falasdinu ba ya mutunta Amurka duk da makudan kudin da ta ke samarwa domin aikin agaji a yankin.

[ad_2]

More News

Atiku ya bayar da tallafin miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri babban birnin...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

Mutanen Sokoto na ta murnar kashe ƙasurgumin ɗanbindigar nan Halilu Buzu

Mazauna yankin Sokoto da kewaye na murnar kashe wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Kachallah Halilu Buzu, da sojojin Najeriya suka yi a farmakin da...