Amurka Ta Kori ’Yan Najeriya 900 Cikin Shekara Shida — Rahoto

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Amurka (ICE) ta bayyana cewa ta kora ’yan Najeriya 902 daga kasar tun daga shekarar 2019 zuwa 2024, kamar yadda rahoton shekara-shekara na hukumar na 2024 ya nuna.

Bugu da ƙari, akwai wasu ’yan Najeriya 3,690 da aka sanya musu takardar kora amma har yanzu suna cikin rudani, suna jiran cikakken aiwatar da hukuncin.

Kodayake adadin korar ’yan Najeriya daga Amurka ya ragu daga 286 a 2019 zuwa 138 a 2024 — raguwar kashi 51.7 cikin ɗari — rahoton ICE ya nuna cewa yawancin korar ta fi yawa ne a farkon mulkin Donald Trump, musamman a shekarun 2018 da 2019, kuma ana sa ran zai ƙaru a 2025 sakamakon sabon matakin ƙara tsaurara dokoki.

Daga dukkan ƙasashen Afirka, Najeriya ce ta fi kowace kasa yawan wadanda aka kora daga Amurka. Senegal ce ke biye da Najeriya da korar mutane 716, sai Ghana da 582, sannan Mauritania da 491.

More from this stream

Recomended