Allah Ya yi wa Magajin Garin Sokoto, Alhaji Hassan Marafa Danbaba rasuwa a ranar Asabar a Kaduna bayan gajeruwar rashin lafiya.
Wata majiya dake kusa da marigayin ce ta bayyana cewa ya mutu ne jin kadan bayan da ya yanke jiki ya fadi.
Ana sa ran za a yi janai’zar mamacin a ranar Asabar a birnin Sokoto.
Marigayin ya kasance ɗa ga Aishatu Ahmadu Bello, wadda ƴa ce ga Sardauna Ahmadu Bello.
Alhaji Hassan Marafa ne Magajin Garin Sokoto na 13 kuma an naɗa shi ne a ranar 31 ga watan Oktoban 1997.