Allah ba zai bari a lalata masarautun Kano ba—Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa sabbin masarautu hudu da gwamnatinsa ta kafa suna nan daram.

Ya bayyana hakan ne a yayin bikin ranar ma’aikata da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha, Kano.

Ganduje ya jaddada cewa Allah ba zai bar kowa ya kawo ƙarshensu ba.

In ba a manta ba, Gwamnan ya raba masarautun Kano gida biyar sannan ya tsige Sarkin Kano na lokacin Alhaji Muhammadu Sanusi.

To sai dai kuma a makon da ya gabata a wani faifan bidiyo da ya fito fili, Sanata Rabi’u Kwankwaso, jagoran jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), ya yi ikirarin cewa gwamnati mai jiran gado ta Engr Abba Kabir Yusuf za ta yi nazari a kan tsige masarautun tare da sauya tsarin masarautar.

A nasa martanin, Ganduje a lokacin da yake kammala jawabinsa a wajen bikin ranar ma’aikata, ya bayyana cewa sabbin masarautun guda hudu na nuni da hadin kai, ci gaba da jin dadin al’umma.

More News

Ribadu ya koka kan yadda jami’an tsaro suke sayarwa da ƴan ta’adda bindigogi

Mai bawa shugaban shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya ce wasu daga jami'an ƴan sanda da kuma sojoji suna ɗaukar bindigogi daga...

Gwamnan Legas Sanwo-Olu ya kara mafi ƙarancin albashi zuwa naira 85,000

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana shirin gwamnatinsa na fara biyan sabon mafi karancin albashi na N85,000 ga ma'aikatan jihar.Sanwo-Olu ya bayyana hakan...

Sama da mutane 100 aka tabbatar sun mutu a gobarar hatsarin tankar mai a Jigawa

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 140 a hatsarin gobarar tankar mai da ta faru a garin Majia dake kan...

Sojoji sun kashe ɗan Boko Haram a Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya na Birged Ta 21 dake aiki da rundunar Operationa Haɗin Kai dake aikin samar da tsaro a yankin arewa maso...