Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Joe Ajaero, ya bayyana cewa idan aka ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayayyaki ba tare da katsewa ba, kungiyar kwadago za ta iya neman sabon mafi karancin albashin da ya kai naira miliyan daya ga ma’aikatan Najeriya.
Ajaero ya ce bukatar kungiyoyin kwadago za ta yi tasiri ne sakamakon tsadar rayuwa da ke karuwa tun lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau karagar mulki, musamman saboda cire tallafin man fetur da wasu manufofi.
Shugaban NLC ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da Arise News, a yammacin Lahadi.
Ya ce, “Wannan naira miliyan dayan na iya yin tasiri idan darajar Najeriya (Naira) ta ci gaba da faduwa; idan aka ci gaba da samun tashin farashin kaya ba tare da la’akari ba domin kuwa bukatar ƴan ƙwadago ta dogara ne da abin da ke faruwa a cikin al’umma.
“Za ku tuna cewa a lokacin da muke tunanin naira 200,000 (a matsayin mafi karancin albashi), farashin canjin dala ya kai N800/N900. Yadda muke magana a yau ɗin nan, farashin canji ya kai kusan N1,400 ko ma fiye da haka.
“Waɗannan su ne batutuwan da ke ƙayyade buƙatu kuma hakan yana shafar tsadar rayuwa. Kuma a kodayaushe muna cewa bukatarmu za ta dogara ne kan tsadar rayuwa. Za ku yarda da ni a yau cewa buhun shinkafa kawai yana kai kusan N60,000/N70,000 ko fiye.”