Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana damuwarsa kan yadda jami’an gwamnati da hukumomin kasar ke kara nuna halin ko-in-kula da gayyatar da Majalisar Tarayya ke yi musu domin amsa tambayoyi.
Akpabio ya bayyana wannan matsaya ne ta bakin Sanata Abdul Ningi a wani taro na kasa kan lissafin kudade da shugabancin al’amuran kudi, wanda kwamitocin kula da asusun gwamnati (PACs) na Majalisar Dattawa da ta Wakilai suka shirya tare a ranar Litinin.
Ya soki yadda hukumomi da dama ke watsi da wannan hakkokin Majalisa, yana mai cewa wajibi ne kwamitocin su sake farfaɗo da ikon duba yadda kudade ke gudana ta hanyar bincike mai zurfi da kimanta amfani da kasafin kudi.
Akpabio ya bukaci a samar da karin goyon bayan fasaha da kuma amfani da na’urorin zamani domin inganta aikin lura da harkokin kudi, musamman a hukumomi masu wahalar sa ido irin su Babban Bankin Najeriya (CBN), Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), da Hukumar Haraji ta Tarayya (FIRS).
A nasa jawabin, Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, wanda Jagoran Majalisa Julius Ihonvbere ya wakilta, ya bayyana damuwa kan raunanan hanyoyin duba lissafin kudi a Najeriya. Ya ce har yanzu akwai tambayoyi na duba kudaden gwamnati da suka haura Naira biliyan 300 da ba a amsa ba.
Abbas ya jaddada cewa dole ne a dakile raina dokokin bita na asusun gwamnati. Ya ce za a ci gaba da daukar mataki kan duk wata sabawa da aka tabbatar.
Ya bayyana cewa Majalisa ta 10 ta rungumi matsaya mai karfi ta hanyar kirkiro hanyoyin sa ido kai tsaye, tsarin bibiyar matakai, da kuma digitizing na duba lissafin kudi domin tilastawa hukumomi su bi doka da oda.
Haka kuma, ya bukaci kafa ingantaccen tsarin kasa daya na duba lissafin kudade domin tabbatar da daidaito a dukkan matakan gwamnati. Ya ce hakan zai ba da damar duba yadda ake aiwatar da kasafin kudi bayan amincewar Majalisa.
Ya bayyana cewa Majalisa za ta ci gaba da aiwatar da duba bisa aiki da sakamako, tantance bangarorin gwamnati, da kuma nazarin tasirin kudade ga al’umma.
Akpabio Ya Koka Kan Yadda Jami’an Gwamnati Ke Watsi Da Gayyatar Majalisa Ke Aika Musu
