
Cikin mambobin kwamitin har da matar mataimakin shugaban kasa Mrs Dolapo Osinbajo
A ranar Litinin ne Shugaba Buhari ya nada mai dakinsa Aisha daya daga cikin mambobin kwamitin.
Malam Garba Shehu shi ne kakakin fadar gwamnati kuma ya shaida wa BBC cewa don an samar da kwamitin ne don magance shaye-shayen muggan magunguna da ke ta karuwa a kasar.
Sai dai fatan mafiya yawan ‘yan kasar shi ne na gannin ayyukan wannan kwamitoci sun kai ga magance matsalar shan abubuwa masu sa maye musamman a tsakanin matasan kasar.
Dalilin zabar Aisha
Malam Garba Shehu ya ce an zabi uwargidan shugaban kasar ta kasance a kwamitin ne saboda ganin irin rawar da take takawa tun farko wajen ganin an yaki shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa a kasar.
“Tun ma kafin gwamntai ta zo da wannan batu, ita Hajiya Aisha ta sha tara matan gwamnoni don neman maslaha kan wannan matsala da ta addabi al’umm,” in ji Garba Shehu.
Sannan a makon da ya gabata ma an ta yada wani bidiyo da aka ji maidakin shugaban kasar na cewa, wasu mutum biyu sun mamaye gwamnatin mijin nata su ke cin moriyar komai.
Su waye sauran ‘yan kwamitin?
Tsohon gwamann soja a jihar Legas Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ne shugaban kwamitin.
Sannan akwai uwargidan mataimakin shugaban kasa Dolapo Osinbajo a cikin kwamitin.
Girman matsalar shaye-sheye
Matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi dai gagrumar matsala ce da ta addabi Najeriya.
Ko a farkon wannan shekarar BBC ta fitar da wani rahoto kan binciken da ta yi a kan matsalar shaye-shaye, inda ta gano hannun wasu kamfanonin sarrafa magunguna.
Hakan ne kuma ya kai ga gwamnatin kasar rufe kamfanonin tare da haramta amfani da sinadarin kodine da ke kara jefa rayuwar matasan kasar cikin hadari.