A jerin maƙalolinmu daga marubuta ƴan Afrika, ƴar jaridar Najeriya kuma marubuciya Adaobi Tricia Nwaubani ta duba ƙarfin ikon Twitter da matakin gwamnatin Najeriya na son kawo karshensa.
Yanzu wata biyu kenan tun da gwamnatin Najeriya ta haramta amfani da Twitter bayan da kamfanin na fasaha ya cire wasu saƙonni da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa inda kamfanin ya ce saƙon ya saɓa dokokinsa na amfani da kalaman ɓatanci.
Duk da ka-ce-na-ce da ya biyo bayan haka a faɗin duniya, ciki har da kausasan kalaman alla-wadai daga manyan jami’an diflomasiyyar ƙasashen waje da ke ƙasar, gwamnatin ta tsaya kan bakanta.
Sai dai ranar Laraba ta sanar da cewa tana gabar ƙarshe ta sasantawa da Twitter kuma za a dage haramcin nan da ƴan kwanaki ko makonni.
Mafi yawan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan haramcin ya mayar da hankali ne kan illar haramcin kan ƴancin bayyana ra’ayi da na tattalin arziki.
Ƴan Najeriya da yawa suna amfani da shafin ne wajen bayyana ɓacin ranzu game da gwamnati da kuma mu’amala da abokan kasuwancinsu.
Amma matakin Twitter na cire saƙon Shugaba Buhari- wanda ya yi barzanar amfani da karfi kan masu iƙirarin ɓallewa daga Najeriya – ya zo a lokacin da bai dace ba. Wannan ya zama wani tushe ne muhawara a sassan duniya, ciki har da Indiya.
Kamfanin na Amurka mai zaman kansa ya nuna kamar yana shiga al’amuran cikin gidan Najeriya ba tare da wani isasshen sani kan tarihinta ba balle ya san abin da matakin nasa zai haifar.
Sabon salon mulkin mallaka
A lokacin, Twitter ya ce sakon na shugaban ya saɓa wa dokokinsa.
Kamfanin na da damar amfani da dokokinsa, amma Shugaba Buhari ya wallafa wannan bayanin ne don isar da sako a matsayinsa na Shugaban Najeriya zuwa ga mutanensa inda ya yi amfani da shafin gwamnati.
Kuma an wallafa sakon a sauran shafukan sada zumunta a fadin ƙasar.
Dai-dai ne wani kamfanin Amurka mai zaman kansa ya samu ikon sauyawa, ba tare da izini ba, sako a hukumance na shugaban wata ƙasa a Afrika da aka zaba ta hanyar demokuraɗiyya? Wannan ba komai ba ne illa tsabar sabon salon mulkin mallaka.
Ƴan Najeriya na da ƴancin sanin shiri da manufofin shugabansu, ko da kuwa kalamansa ba su dace ba. Suna da ƴancin sani idan yana shirin kai masu mummunan hari.
Haka kuma, ƴan Najeriya na da ƴancin mayar masa da martani a wani ɓangare na sadarwa tsakanin gwamnati da ƴan ƙasarta.
Saƙonnin Buhari sun yi barazanar ɗaukar mataki kan ƴan ƙungiyar IPOB ta ƴan ƙabilar Ibo, wadda ke koƙarin ɓallewa daga Najeriya.
An haramta IPOB a shekarar 2017 – kungiyar ta kai ƙarar gwamnati kotu kan haramcin kuma ba ta yi nasara ba.
Ruruwa wutar rarrabuwar kai
Yayin da ƴan ƙabilar Ibo da dama ke tunanin ana ware su ta hanyoyi da dama, kamar hana su muƙamai masu muhimmanci a gwamnati, mafi yawansu ba sa goyon bayan muradin Ipob na ɓallewa.
Haka kuma ba sa son tashin hankalin da suke assasawa da sauran ƙabilu- waɗanda shugaban ipob Nnamdi Kanu ke yawan kira da dabbobin dawa.
A watan Fabrairu, Facebook ya rufe shafin Nnamdi Kanu saboda kalaman nuna ƙiyayya amma ya ci gaba da amfani da shafin Twitter.
Goge saƙonnin Buhari, Twitter ya nuna cewa yana goyon bayan Ipob kuma magoya bayan kungiyar ba su bata lokaci ba wajen murnar abin da suka fahimta a matsayin goyon bayan Twitter.
Bayan da gwamnati ta soki wannan lamari a watan Yuni, Twitter ya cire kaɗan daga cikin saƙonnin shugaban Ipob ɗin.
Haka kuma, shigar Twitter lamarin Najeriya ya rura wutar rarrabuwar kai da ya haifar da zanga-zangar #EndSars ta watan Oktoban 2020 da aka yi kan cin zarafin da ƴan sanda ke yi.
Ƙungiyoyi daban-daban sun shiga cikin shirya zanga-zangar da aka fara ta intanet kafin daga bisani aka ci gaba a kan tituna a faɗin Najeriya tsawon kusan mako biyu.
Amma lokacin da Twitter ya sanya shuɗin maki mai nuna alamar ‘verified’ a kan shafin ɗaya daga cikin ƙungiyoyin amma bai sa a wasu ba, hakan ya haifar da hamyya mai ƙarfi a tsakaninsu kuma wasu sun janye gaba ɗaya ma daga gangamin.
“Cikin rashin sani, Twitter ya zaɓi shugabannin wannan gangami a Najeriya kuma ya ƙara rura hamayyar da dama ta fara raba kawuna masu shirya gangamin,” a cewar ɗan jaridar Najeriya Ohimai Amaize.
Ƙoƙarin hana yin suka
Kamfanin fasahar ya shiga gonar da ko ƙwararrun jami’an diflomasiyyar ƙasashen waje da shugabannin ƙasashe ke tsoron shiga.
Mutanen waje sun fahimci cewa bai dace su yi gaggawar tsoma baki a harkokin ƙasashen Afrika ba, kamar Najeriya, inda matsalolinta suke da yawa fiye da tsammani.
Suna ci gaba da ɗora alhakin yin wannan kan kungiyoyin ƙasar da suka fi su fahimtar yadda abubuwa ke tafiya a ƙasar.
Matakin Twitter na kafa hedikwatarsa na Afrika ta Yamma a Ghana mataki ne na ƙara samar da fahimtar al’adu.
Sharuɗɗan gwamnatin Najeriya na ɗage haramcin sun ƙunshi sai Twitter ya yi rajistar kamfaninsa a Najeriya kuma wasu daga cikin ma’aikatansa su zauna a ƙasar.
Gwamnatin Buhari ta nuna rashin girmama dokar ƙasa da ƴancin bayyana ra’ayi, inda aka tsare wasu ƴan jarida da masu fafutuka don kawai sun soki gwamnati.
Haramta amfani da Twitter gaba ɗaya wani yunƙuri ne na gwamnati na toshe bakin masu suka kuma ƴan Najeriya na da hujjar damuwa game da haka.
Amma yadda babban kamfanin fasahar ya ɗauki matakin yanke hukuncin wanda zai yi magana kuma a wane lokaci, abin damuwa ne.
Wannan na cin karo da ƴancin bayyana ra’ayi, a lokacin da ake tsananin buƙatar muhawara a bayyana a ƙasar da ke aiki da demokuraɗiyya.
Idan matakin gwamnatin Najeriya na haramta amfani da Twitter alama ce ta kama-karya, lallai abin ɗaga hankali ne a ce wani Ba’amurke zaune kan kujerarsa ta alfarma a yankin Silicon Valley ya tsoma bakinsa cikin harkokin cikin gidan ƙasa mai ƴancin kanta a nahiyar Afrika.