Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwasu ya ce ya zabi tsayar da tsohon kwamishinansa na ayyuka, Abba Kabiru Yusuf domin yin takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PDP ne domin gudun kar a maimaita abin da magajinsa Abdullahi Umar Ganduje ya yi musu na cin amana.
A wata hira da ya yi da BBC jagoran na Kwankwasiyya ya ce a shekara ta 2015 sun duba mutumin da ya fi kowa shekaru da girma da mukami wajen tsayar da dan takarar gwamnan jihar, inda suka ba wa Ganduje, da zaton cewa za a zauna lafiya ba za a yi butulci ba da cin amana, kuma za a yi wa jama’a aiki amma kuma sai suka samu sabanin haka.
Kwankwaso ya ce bayan nazari da tuntuba da shawara da suka yi da mutane da dama tsawon shekara uku da doriya domin duba wanda ya kamata su tsayar a takara ba tare da an sake maimaita abin da ya faru ba na sabani da matsalolin da suka samu kansu a ciki, kuma yawanci suka nuna cewa Abba K. Yusuf ne ya fi dacewa.
Sanatan ya ce wanda suka yanke shawarar tsayarwar wanda shi ne kwamishinan ayyuka a lokacin gwamnatinsa ta wa’adi na biyu, shi ne ya jagoranci dukkanin ayyukan cigaba da aka yi a jihar a lokacin, wadanda suka hada da gadojin sama da na kasa da sabuwar jami’ar jihar (North-West a da), da dukkanin manyan makarantun jihar, da ayyukan rukunan gidajen da ada ake kira Kwankwasiyya da Amana da Bandurawo.
Ya ce yana bakin ciki da watsi da gwamnatin jihar ta yanzu ta yi da wadannan ayyuka, amma Abba ya fi shi bakin ciki a kai, don haka yana ganin idan har ya samu hawa kujerar gwamnan za a raya wadannan ayyuka, a kuma dora a kai.
Game da maganar da wasu ke yi cewa ya tsayar da Abban ne saboda sirikinsa ne, tsohon gwamnan ya ce abin ba haka yake domin ba ya auren ainahin ‘yar da shi Kwankwason ya haifa, amma kasancewar gidansu babban gida ne kuma gidan sarauta yana da dangi da ‘yan uwa da iyaye mata da ‘ya’ya da jikoki, ya kara da cewa, ”kuma ba za ka hana wani ya ce yana so zai aura, kuma idan wani ya aura daga ciki ba za ka ce da shi a’a me ya sa ka aura ba.”
Sannan ya ce, ”kuma wannan ba zai kamata ya zama wata matsala a kan cewar wanda ya yi aure a cikin family (iyali) dinka ka ce wata dama ta zo za ka hana shi, abin da ba a so shi ne ka fitar da shi kan son zuciya, amma babban abin da yake akwai shi ne kowa ya san halinsa kowa ya san aikinsa, to wannan su ne ginshikai.”
Jagoran na Kwankwasiyya ya kuma yi wani shagube da cewa: ”A siyasa abin da ba a so shi ne, ko daga ina ka auro mata ba wani abin damuwa ba ne, amma babbar matsala ita ce, in ka zo ka zama mijin-hajiya, in ka zo ka kawo tsari wanda ike ita ce take mulki ba kai ba,
kuma Abban nan matansa biyu ne, kuma mu da muke da mata dai-dai mun sani cewar wanda yake da mata biyu a irin wannan yanayi na mace tazo ta ce sai abin da take so a gida to ba kamar na me mace daya ba ne.’
Dangane da maganar da wasu ke yi cewa wanda ya tsayar takarar ba shi da farin-jini, ba a san shi sosai ba, kuma yana da girman-kai, Kwankwason ya ce lamarin ba haka yake ba, domin Abba a cewarsa aikinsa kawai yake sanyawa a gaba, domin mutum ne da ba za ka gan shi a guri na ashsha ba, saboda haka abin da ake so shi ne aiki da rike amana da gaskiya da sauran abubuwa wadanda za su taimaka wa jihar kano.
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ya san tsohon mataimakin gwamnan jihar na kwanan nan Farfesa Hafizu Abubakar tun sama da shekara 40.
Kuma duk wata dama da ya samu ta ya taimaka masa ya taimaka masa kuma zai ci gaba da taimaka masa, ba fada suke yi ba, ya ce, amma abin da aka ce da shi, shi ne ya nemi kujerar sanata da Kwankwason yake kai a yanzu amma Farfesan bai nuna sha’awa ba, kamar yadda shi ma Mallam Salihu Sagir Takai, aka nemi ya yi takarar kujerar sanata ta Kano ta Kudu amma ya ki.
Sanatan ya kuma ce maganar da wasu ciki har da wasu da aka ce ‘yan tafiyarsa ta Kwankwasiyya ne ke yi ta cewa matakin da suka dauka na tsayar da Abba Kabiru Yusuf takara zai ba wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na APC damar cin zabe a saukake, ya ce wannan sharrin makiya ne, kuma idan ma was nasa sun fadi hakan to ai ba su ne mutanen Kano ba.