Abdul Samad Rabiu BUA Ya Yi Wa ‘Yan Wasan Najeriya Alƙawarin Kyautar Kuɗi Kafin Wasan Moroko

Shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya yi wa ‘yan wasan ƙasar nan alƙawarin tallafin kuɗi domin ƙarfafa musu gwiwa gabanin wasansu da ƙasar Moroko da za a fafata ranar Laraba.

Rabiu ya bayyana cewa zai ba su dala miliyan ɗaya idan har suka lashe kofin gasar, sannan kuma zai ba su dala 100,000 kan kowace ƙwallon da suka zura a wasan ƙarshe.

Ya ce wannan alƙawari na da nufin ƙara wa ‘yan wasan ƙwazo da jajircewa domin su bai wa ƙasa nasara a gasa mai muhimmanci.

More from this stream

Recomended