A Jawabin Babbar Sallah Shugabannin Jihar Niger Sun Kira A Zauna Lafiya

[ad_1]

Shugabannin jihar Niger sun yi anfani da jawaban bukukuwan sallah wajen fadakar da al’umma mahimmancin zaman lafiya tsakanin jama’a.

A sakonsa ga al’ummar masarautarsa, Mai Martaba Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Sa’idu Namaska, yayi kira ga matasa, musamman a wannan lokacin na hada hadar siyasa, da kada su bari ‘yan siyasa su yi anfani dasu wajen aikata abun da zai tayar da hankalin jama’a.

Shi ma gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello, a nasa jawabin ya kara yin bayani akan mahimmancin zaman lafiya. Ya ce “muna bukatar ku gudanar da bukukuwan sallah cikin natsuwa da kwanciyar hankali domin dorewar zaman lafiya saboda sai da shi ne ake samun ci gaban kasa ko ta wace fuska.”

Gwamnan ya kara da cewa ana bukatar kowa ya bi doka wajen gudanar da harkokin siyasa musamman a wannan lokaci da ake tunkarar babban zaben shekarar 2019. Ya taya jama’ar jiharsa da ma Nigeria gaba daya murnar babbar sallah.

Su ma malamai ba’a barsu a baya ba, saboda sun gudanar da nasu nasihohin a lokacin sallar idin. Shugaban malaman IZALA a jahar ta Niger Shaikh Aliyu Adarawa, ya yi tsokaci ne akan dambarwar da aka samu game da ganin watan Shawwal tare da kiran Fadar Sarkin Musulmi, ta yadda da rahotanni daga dai dai kun jama’a gameda ganin-wata, a hada shi da ayyukan kwamitin fatawa na kasa kada ya tsaya Sokoto kawai.

A jihar Niger an gudanar da sallar a koina cikin kwanciyar hankali da walwala.

A saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

[ad_2]

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya Æ™irÆ™iri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a Æ™ara wa Æ´an bautar Æ™asa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...