Wata babbar kotu dake birnin Fatakwal da mai shari’a Chiwendu Nwogu ke jagoranta a ranar Laraba ta rushe shugabancin jam’iyyar APC na jihar da Ojukaye Amachree ke jagoranta.
Kotun ta kuma soke zaben fidda gwanin takarar gwamnan jihar da Tonye Cole ya lashe inda ta ce zaben da aka yi masa ya sabawa kundin tsarin mulki.
Haka kuma kotun ta soke zabukan fidda gwani na yan majalisar wakilai ta tarayya, yan majalisar dattawa da kuma na yan majalisar dokokin jihohi da jam’iyar ta gudanar a jihar Lagos.
Har ila yau kotun ta kuma soke zaben shugabannin jam’iyar na mazabu da kuma na kananan hukumomi da shugabancin jam’iyyar ya gudanar.
Wasu mutane ne suka shigar da kara gaban kotun suna kalubalantar yadda aka gudanar da zabukan shugabannin jam’iyar inda suka ce zabukan sun saba sharuda da kuma kundin tsarin mulkin jam’iyar PDP.