10.3 C
London
Thursday, November 7, 2024
HomeHausaNajeriya Ta Cikin Jerin Kasashen Da Al’umominsu Ke Fama Da Talauci

Najeriya Ta Cikin Jerin Kasashen Da Al’umominsu Ke Fama Da Talauci

Date:

Related stories

Ƴansandan Najeriya sun hallaka ƴan fashi a Abuja

Rundunar 'Yan sandan Birnin Tarayya ta kashe wasu ‘yan...

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...
spot_imgspot_img

Wani rahoton kungiyar bincike da kididdiga akan matakin talauci a duniya, ya nuna cewa Najeriya a yanzu, ta kasance babbar cibiyar fatara da matsanancin talauci a duniya, mukamin da ta ture kasar Indiya ta dare a kai.

Rahoton ya bayyana cewa kimanin adadin ‘yan Najeriya miliyan 87, da ke wakiltar kusan kashi 50 cikin 100 na yawan jama’ar kasar, suna rayuwa ne a cikin matsanancin talauci, musamman ma a yankunan karkara.

A baya-bayan nan ma, kididdiga ta nuna cewa jihohin Arewacin Najeriya, su ne suka fi yawan matalauta a duk duniya, da adadinsu ya kai kashi 85 cikin 100 na jama’ar yankin.

Wannan yanayi dai na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatoci a Najeriya suke da’awar fitowa da tsare-tsare masu manufar yaki da fatara da samar da ayukan yi, wadanda manazarcin lamurran siyasa da tattalin arziki, Dr. Mansur Isah Buhari, yake ganin basu yi wani tasiri ba.

Wannan sabon matsayi na talauci a Najeriya, ya saka shakku da tababar samun nasarar muradun wanzar da ci gaba na Majalisar Dinkin Duniya, na kai karshen matsanacin talauci ya zuwa shekara ta 2030, a dai dai lokacin da kuma ake fargabar lamarin zai fi Kamari ya zuwa shekara ta 2050, sa’adda ake hasashen samun karuwar yawan jama’a a kasar.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here