Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi kira ga dukkan ƴan ƙasarta da ke zaune a Venezuela da su gaggauta barin ƙasar, sakamakon tabarbarewar tsaro.
Ma’aikatar ta ce ta samu rahotannin cewa wasu ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai sun fara tare hanyoyi a wasu sassan ƙasar, inda suke tsayar da ababen hawa tare da binciken motocin Amurkawa da kuma na mutanen ƙasashen da ke goyon bayan Amurka.
Wannan sanarwa na zuwa ne mako guda bayan sojojin Amurka sun kai hari Venezuela, inda suka kama shugaban ƙasar Nicolas Maduro da matarsa, suka tafi da su Amurka, tare da gurfanar da su a gaban kotu.
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa a halin yanzu Amurka ce ke taka rawa wajen jagorantar al’amuran ƙasar tare da haɗin gwiwar gwamnatin rikon ƙwarya.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa har yanzu makusantan Maduro ne ke ci gaba da riƙe iko da jami’an tsaron ƙasar.
Amurka Ta Bukaci Ƴan Ƙasarta Su Fice Daga Venezuela Cikin Gaggawa

