An Kammala Binne Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a Daura

An binne tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, a gidansa da ke Daura, jihar Katsina, da misalin ƙarfe 5:50 na yamma, a ranar Lahadi 13 ga watan Yuli, 2025.

Buhari ya rasu ne a birnin Landan da ke Birtaniya bayan doguwar jinya. Ya rasu yana da shekara 82 a duniya, shekaru biyu bayan sauka daga kujerar mulki.

Tsohon shugaban ya fara jagorantar Najeriya a matsayin soja daga watan Disamban 1983 zuwa Agustan 1985, kafin a kifar da gwamnatinsa ta soji. Sai dai bayan fiye da shekaru 30, ya sake dawowa kan mulki ta hanyar dimokuraɗiyya, inda ya kayar da shugaban kasa na wancan lokaci, Goodluck Jonathan, a zaben 2015.

An rantsar da shi a matsayin shugaban farar hula a ranar 29 ga watan Mayu, 2015, inda ya yi mulki na tsawon wa’adi biyu har zuwa 29 ga Mayu, 2023.

Tun farkon mulkinsa na farar hula, Buhari ya fuskanci matsalolin lafiya, lamarin da ya sa ya riƙa kai-komo tsakanin Najeriya da Landan domin samun kulawar likitoci. Masana da masharhanta sun bayyana cewa hakan ya shafi tasirinsa wajen gudanar da al’amuran mulki. A gefe guda kuma, masu suka sun zargi gwamnatinsa da ɓoye irin rashin lafiyar da ke damunsa.

Buhari ya rasu ya bar mata ɗaya, A’isha Buhari, da ‘ya’ya goma.

More from this stream

Recomended