Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya samu sabon mukami a hukumomin gwamnatin tarayya, kwana kalilan bayan murabus dinsa daga shugabancin jam’iyyar APC a matakin kasa.
Ganduje ya samu nadin ne a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN), kamar yadda aka bayyana a wani biki na kaddamar da sabbin shugabannin hukumar a birnin tarayya Abuja.
Nadin nasa ya zo ne mako guda bayan da ya ajiye mukaminsa a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, yana mai cewa dalilan murabus din nasa sun ta’allaka ne da “muhimman batutuwa na kashin kai.”
Jam’iyyar APC ta maye gurbinsa da Ali Bukar Dalori wanda yanzu ke matsayin sabon shugaban jam’iyyar a matakin ƙasa.
Ana sa ran sabon mukamin da Ganduje ya samu zai bai wa gwamnatin tarayya damar amfani da kwarewarsa a fannin shugabanci da tsara manufofi, musamman a bangaren sufurin jiragen sama.
Ganduje Ya Samu Sabon Mukami Bayan Murabus Daga Shugabancin APC
