Tsohon Antoni Janar, Abubakar Malami, Ya Fice Daga APC, Ya Koma Jam’iyyar ADC

Tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki, tare da bayyana komawarsa jam’iyyar ADC.

Malami ya bayyana sauyin jam’iyyar ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 2 ga Yuli, 2025, inda ya ce matakin ya biyo bayan shawarwari da zurfin tunani da ya yi kan halin da kasa ke ciki.

A cewarsa: “Bayan shawarwari da zurfin nazari, na yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar APC tare da rungumar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), jam’iyyar da ke da burin ceto Najeriya daga ci gaba da tabarbarewa.”

Malami ya zargi gwamnati da watsi da al’umma, yana mai cewa rashin tsaro ya mamaye arewacin Najeriya, yayin da farashin abinci ya ninka sau uku.

Ya ce: “Najeriya na jini. Rashin tsaro ya shafi gidajenmu, musamman a Arewa. Fashi, garkuwa da mutane da ta’addanci sun zama ruwan dare. Gwamnati na fifita siyasa a kan tsaron rayukan ’yan kasa.”

Ya kuma ce: “Tattalin arzikinmu ya tabarbare. Talakawa sun kasa ciyar da iyalansu. Ayyuka na bacewa. Matasa sun rasa fata. Gwamnati na yin kage maimakon samar da mafita.”

Malami ya bayyana ADC a matsayin jam’iyyar da ta ginu kan gaskiya da adalci, yana mai bukatar hadin kan ’yan Najeriya don ceto kasar.

Ya kuma jaddada cewa: “Ba zan taba barin mutanen Jihar Kebbi ba. Wannan sauyi domin kare muradunku ne da dawo da fata ga makomar mu.”

Ya kammala da kira ga al’umma da su hada kai: “Mu tashi tsaye mu kwato Najeriya. Kasar nan tamu ce gaba ɗaya.”

Sauyin da Malami ya yi na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun sauyin sheka gabanin zaben 2027.

More from this stream

Recomended