Atiku, Obasanjo, Gowon, Shettima da El-Rufai Sun Hadu a Taron Bikin Ranar Haihuwar Mu’azu

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya halarci taron tunawa da cika shekaru 70 da haihuwa na tsohon gwamnan Jihar Bauchi kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu, a ranar Asabar.

Taron ya samu halartar manyan fitattun shugabannin Najeriya da suka hada da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, mataimakin shugaban kasa mai ci, Kashim Shettima, tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Sauran mahalarta sun hada da shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da wasu sanannun ’yan siyasa da shugabannin al’umma daga sassa daban-daban na kasar.

A wani sakon da Atiku ya wallafa a shafinsa na X (tsohon Twitter), ya bayyana cewa ya yi aiki tare da Mu’azu daga shekarar 1999 zuwa 2007 domin gina tubalin kyakkyawan shugabanci da ci gaban tattalin arzikin Najeriya ta hanyar karfafa bangaren masu zaman kansu.

More from this stream

Recomended