Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja da yammacin Asabar.
Cikin waɗanda suka halarci wannan taro akwai tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose; tsohon gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom; da tsohon gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu.
Wani majiya da ya halarci taron ya shaida cewa: “Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose, Ministan FCT Nyesom Wike, Shugaba Bola Tinubu, tare da tsoffin Gwamnonin Jahohin Benue da Abia wato Samuel Ortom da Okezie Ikpeazu sun gana da shugaban ƙasa a fadar Villa da ke Abuja a yau.”
Sai dai har zuwa lokacin da aka fitar da rahoton, babu cikakken bayani game da abin da suka tattauna a yayin taron.
A ranar 9 ga Yuni, yayin hutun Sallah, Fayose ya kai wa Shugaba Tinubu ziyara a gidansa da ke Legas. Bayan ganawarsu, Fayose ya bayyana wa manema labarai cewa ziyarar tasa na ƙarfafa gwiwar shugaban ƙasa ne.
A cewarsa, “Ko a lokacin da nake gwamna karkashin jam’iyyar PDP, na riƙa ganin cewa Tinubu shugaba ne nagari kuma na gaskiya.”
Fayose ya kuma ƙara da cewa Shugaba Tinubu ya cancanci yabo saboda yadda yake ƙoƙarin daidaita tattalin arziƙin ƙasar nan.
Har yanzu dai ana ci gaba da hasashe kan ma’anar wannan ganawa da tasirinta a siyasar Najeriya, musamman ganin cewa manyan jiga-jigai daga jam’iyyar adawa ne suka halarta.
Taro a Fadar Shugaban Ƙasa: Tinubu Ya Karɓi Baƙuncin Wike, Fayose, Ortom da Ikpeazu a Abuja
