Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan Biyu Da Tirela 20 Na Shinkafa Ga Wadanda Ambaliya Ta Shafa a Neja — Shettima

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da bayar da gudummawar kuɗi har naira biliyan biyu da kuma tirela 20 na shinkafa domin tallafawa al’ummar da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Neja.

Shettima ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar jaje da ya kai garin Mokwa, daya daga cikin wuraren da ambaliyar ta fi shafa, inda ya ce gwamnatin tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen magance matsalolin da suka dabaibaye rayuwar mazauna yankin.

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta gyaran gadoji da sauran muhimman ababen more rayuwa da ambaliyar ta lalata a jihar.

Rahotanni daga hukumomin ceto sun tabbatar da mutuwar sama da mutum 200 a ƙaramar hukumar Mokwa sakamakon ambaliyar, tare da karin mutum fiye da 500 da har yanzu ba a san inda suke ba — abinda ke ƙara tayar da ƙayar baya dangane da yawan adadin waɗanda suka rasa rayukansu.

More from this stream

Recomended