Dakarun tsaro na Najeriya sun kashe akalla ‘yan bindiga 45 a wani samame da suka kai kusa da garin Kuchi da ke karamar hukumar Munya a Jihar Neja.
Wani masani kan yaki da ta’addanci kuma mai sharhi kan tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X (tsohon Twitter) a ranar Laraba.
A cewar Makama, samamen ya gudana ne da hadin gwiwar jami’an rundunar Sojojin Najeriya da kuma ma’aikatan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), a safiyar Litinin.
Ya ce bayanan sirri sun nuna cewa ‘yan bindigar da aka kashe na daga cikin mabiya Dogo Gide, wani shahararren shugaban ‘yan ta’adda da ke addabar arewacin kasar. An ce ‘yan ta’addan sun fito ne daga dajin Bilbis da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara da kuma wasu maboyarsu a jihar Kaduna, domin kai farmaki a kusa da Kuchi.
“Adadin ‘yan bindigar da suka taru ya haura 100, kuma sun fito ne daga maboyarsu a Zamfara da Kaduna,” in ji Makama, yana nuni da wani majiya da ya nemi a sakaya sunansa.
Makama ya kara da cewa dakarun tsaro sun yi artabu mai tsanani da ‘yan ta’addan a wajen garin Kuchi, inda suka kashe mafi yawan su – fiye da 45 – yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Bincike ya kuma tabbatar da cewa an kwato babura masu yawa da makamai daga hannun ‘yan ta’addan.
Sai dai kuma, rahoton ya bayyana cewa jami’an DSS guda biyar sun jikkata a lokacin musayar wuta, kuma ana kula da lafiyarsu a wani asibiti da ba a bayyana ba.
Sojoji da DSS sun hallaka ‘yan bindiga 45 a Jihar Neja
