Ayyuka Sun Tsaya Cik A Kano Sanadiyar Yajin Aikin Ma’aikata

Yanzu haka dai ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jiha dana tarayya kana da makarantu da asibitoci da galibin kamfanoni masu zaman kansu sun kasance a rufe a birni Kano da kewayen.

Haka zalika zirga zirgar Jama’a ta takaita, musamman a yankunan da bankuna ke hada hadar su.

Tuni dai jami’an kungiyar kwadago a Kano suka yaba da yadda ma’aikatan a kowane mataki suka bi umarnin kungiyar na kasa.

Comrade Kabiru Ado Minjibir shine shugaban reshen jihar na kungiyar ta NLC a jihar Kano ya ce ba’a taba yajin aiki da aka samu kyakyawar biyayya daga ma’aikata irin wannan ba. Ya ce duk kungiyoyin kwadagon uku sun tafi da murya daya. Ya godewa ma’aikatan tare da cewa su ci gaba da zama gidajensu har sai sun ji daga garesu.

Yajin aikin gargadin na zuwa ne a dai dai lokacin da al’umma ke tsaka da matsin tsadar rayuwa, al’amarin daya sanya masu kula da lamura ke ganin matakin zai kara jefa rayuwar jama’a cikin karin garari.

Kabiru Minjibir ya ce ba son ransu ba ne a je yajin aiki saboda shi ne makami na karshe ga kowane shugaban kungiyar kwadago. Dalili ke nan suka ba da wa’adin kwana 14 kafin fantsama cikin yajin aikin domin hankalin gwamnati ya kwanta ta san abun yi cikin wa’adin. Amma ma’aikata sun yi hakuri kimanin shekara biyu da ya kamata a daidaita batun albashi mafi kankanci.

A jihar Jigawa ma,bata canja zani ba, domin ofisoshin gwamnatin tarayya da na jiha sun kasance a rufe, yayin da hada hadar bankuna ta tsaya cik baya ga tsayawar harkokin koyo da koyarwa a makarantun jihar.

Wasu daga cikin Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum dai na ganin kamata yayi kungiyar kwadago ta matsa lamba ga gwamnati kan bukatar kyautata tattalin arziki maimakon karawa ma’aikata albashi.

To amma comrade Aliyu Abubakar Getso tsohon sakataren kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano na cewa ba kasafai gwamnati ke jawo shugabannin kwadago shiga harkokinta na gudanarwa ba, musamman ka alamuran da suka shafi tattalin arziki duk da cewa cikin shugabannin ‘yan kwadagon akwai wadanda suke da cikakken ilimi akan harkokin tattalin arziki. Suna rubutu a kai suna kuma gabatar da kasidu su nuna wa gwamnati irin abun da yakamata ta yi.

Jimlar Naira dubu 65 ne kungiyar kwadagon ta Nigeria ke muradin ya zama mafi karancin albashi a kasar maimakon Naira dubu 18, kodayake har yanzu akwai wasu jihohi da ba sa biyan hakan fiye da shekaru biyar bayan amincewa da dubu 18 a matsayin mafi karancin albashi a Nigeria.

More from this stream

Recomended