Abin da ya sa mutane ke ƙaura daga Borno zuwa Yobe

Bayanan sauti
Rahoton Raliya Zubairu

Bayanai daga Yobe a arewa maso gabashin Najeriya na cewa mutane da dama na ci gaba da isa wasu manyan garuruwan jihar, bayan tserewa hare-haren wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, a yankunan kan iyaka tsakanin Borno da Yobe.

Rundunar ‘yan sandan Yobe ta ce ta lura da yadda mutane da dama da suka fito daga Gubio da Magumeri da Kaga da kuma Konduga a jihar Borno suke kwarara.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar waɗanda kan far wa ƙauyuka, sukan je ne a kan babura, inda suke sace dukiya da kuma mutane.

Wata mata da ta tsere daga yankin Kudancin Geidam ta shaida wa BBC cikin harshen Kanuri cewa mutanen na ɗauke da miyagun makamaki kuma suna kama mutane domin neman kuɗin fansa.

Ta ce wannan lamari shi ya sa suka tsere daga yankinsu suka shiga cikin gari. Ta ce ba za ta iya tantance ko mutanen ƴan Boko Haram ne ko ɓarayi ba saboda suna musu barazana da wuƙaƙe da bindigogi.

A cewar randunar ƴan sandan, ta fara gudanar da bincike kan dalilin da ya sa mutane suke ƙaura kuma ta ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron lafiyar al’umma.

Kazalika, a yankin arewa maso yammacin Najeriya ma matsalar tsaron ce inda mutanen yankin ƙaramar hukumar Goronyo a jihar Sokoto suka ce suna cikin fargaba da tashin hankali saboda ƙaruwar hare-hare da sace-sacen mutane da ‘yan bindiga ke yi.

Shaidu sun ce an kashe mutum biyu yayin da aka sace mutum goma sha biyu da kuma shanu cikin kwana uku jere a wasu ƙauyuka da kuma cikin garin na Goronyo.

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ba ta ce uffan ba, game da ƙorafin yawan hare-haren.

Amma wani da ya nemi BBC ta ɓoye sunansa ya bayyana cewa hare-haren ba iya ƙauyuka suka tsaya ba har da garin Goronyo.

Ya ce ɓatagarin sun shafe kusan sa’a uku suna kai hare-hare a yankin an Goronyo inda suka kai hari gidan wani tsohon ɗan majalisar jiha tare da harbinsa sannan suka yi awon gaba da ƴaƴansa biyu da ƙanwar matarsa.

More from this stream

Recomended