
Asalin hoton, TWITTER/BASHIR_AHMAD
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bukaci shugabannin addini da sarakunan gargajiya da su taimaka wajen wayar da kan jama`a kan riga-kafin cutar korona.
Shugaban ya bayyana haka ne a ganawar da ya yi da ‘yan majalisar koli da ke kula da harkokin addinin musulunci a Najeriya, NSCIA karkashin jagoranci mai alfarma sarkin musulmi, sultan Abubakar Sa’ad ranar Alhamis.
Dama dai a ranar Laraba ne NSCIA din ta shirya wani taron wayarwa malamai da sarakuna kai kan allurar riga-kafin ta korona tare da ma’aikatar lafiya ta kasa kuma sarkin Musulmin ya halarci taron.
Don haka ana iya cewa faduwa ta zo dai-dai da zama don kuwa shugaba Buhari ya bayyana muhimmancin shugabannin addini wajen wayar da kan jama`a ta yadda za su fahinci cewa ana yi ne domin kare lafiyarsu.
Ya jaddada cewa suna daga cikin mutanen da za su sa allurar riga-kafin ta samu karbuwa.
Tun bayan da sanarawar samar da allurar riga-kafin korona ta bayyana ‘yan Najeriya ke muhawara kan sahihancinta.
Yayin da wasu ke ganin an yi gaggawar samar da ita, wasu gani su ke akwai lauje cikin nadi daga ƙasashen Yamma wanda mafi yawa su ne suka samar da allurar.
Haka kuma, akwai rukunin mutanen da ke tababa akan ita kanta cutar ta korona inda suke cewa babu ita a zahiri.
Don haka har yanzu ‘yan Najeriya da dama ba su gamsu a kan riga-kafin ba.
Najeriya na daya daga cikin kasashen Afrika da har yanzu ba a fara bayar da allurar ba duk da cewa kasashen da suka ci gaba suna ta bai wa ‘yan kasarsu allurar.
A wannan makon ne kuma Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da samo allurar guda milyan 400 baya fa sama da miliyan 200 da a baya ta samo kuma ta yi alkawarin raba wa kasashen nahiyar.
Shugaba Buhari ya buƙaci su ci gaba da fadakar da al`umma a kan muhimmancin bin ka`idojin kariya da likitoci ke gicciyawa game da cutar kamar wanke hannu da sabulu da ba da tazara.
Asalin hoton, TWITTER
Baya ga batun allurar riga-kafin cutar korona, Shugaban kasar lissafa wasu illolin da ke tattare da rura wutar kabilanci da banbancin addini a kasar.
Ya ce matsalar ce ba ta barin kasa ta ci gaba kuma gwamnatinsa ba za ta bari irin wadannan bambance-bambancen su yi tasiri a cikin tsare-tsare da manufofinta ba.
Dangane da matsalar tsaro kuwa, wadda ta ki ci ta ki cinyewa, shugaba Buhari ya ce gwamnati ba ta sare ba ko kadan.
Ya ce abin take yi ma shi ne samar da kayan yaki ga jami`an tsaro, tare da bin hanyoyin da suka dace wajen kara musu kwarin-gwiwa.
Duk da kalubale daban-daban da gwamnati ke fuskanta, shugaban kasar yace gwamnati ta fito da shirye-shirye na samar da walwala ga rayuwar `yan Najeriya.
Baya ga shirye-shirye da aka sani irin su N-power da adashen-gata na cash transfer, yanzu gwamnati ta bijiro da wani sabon shiri da zai magance ragaitar da yara da `yan mata ke yi suna guje wa makaranta.