Yadda ake gudanar da masarautar Hausawa a Turai

Bayanan bidiyo,
Sarkin Hausawan Turai, Alhaji Sirajo Labbo

Latsa wannan alamar lasifika da ke sama domin kallon Sarkin Hausawan Turai.

Sanye da alkyabba da zabbuni da kuma rawani mai kunne biyu tare da sandan girma, za ka rantse Alhaji Sirajo Jan Kado Labbo dan sarki ne a birnin Kano ko Katsina ko Daura ko Zazzau ko Rano ko Gobir ko kuma Birom inda ‘ya’yan sarki ne kawai ke yin kunne biyu.

To sai dai Alhaji Sirajo shi ne Sarkin Hausawan Turai da ke da babbar fada a birnin Paris na kasar Faransa, wani wuri da watakila ba za a taba tunanin Hausawa za su iya daga kai ba ballantana har ma su kafa masarauta.

Sarkin Hausawan Turai, Alhaji Sirajo Jan Kado Labbo ya ce ba kamar yadda ake yi wa Hausawa mummunar fahimta ba dangane da irin kananan sana’o’in da suke yi musamman a wasu kasashe, Hausawan Turai mutane ne masu kima wadanda suke taimakawa wajen cigaban tattalin arzikin kasashen da suke zaune.

Alhaji Sirajo ya kara da cewa “kasancewarmu ‘yan boko da masu hannu da shuni muna taka rawar azo a gani ta fuskar tattalin arzikin nahiyar Turai. Misali ni ina da kamfanin sadarwa da nake tafiyar fiye da shekara 20 a kasar Faransa. Kuma muna daukar ma’aikata.”

Inganta al’adun Bahaushe a Turai

Dangane kuma da abin da ya shafi al’adar malam Bahaushe, Sarkin na Hausawa ya ce suna yin duk abin da ya kamata wajen ganin al’adu da ma harshen Hausawa bai bata ba musamman a tsakanin yaran da suke haihuwa a can.

An hakkake dai cewa yawon cirani na da tasiri ga al’adu da harshen mutane, inda lokaci da dama wadanda suka bar kasarsu kan haifi yara a wata kasar kuma al’adun kasar su yi tasiri a kan ‘ya’yan nasu.

Kuma harshe da al’adar Hausawa ma dai ba ta tsira ba daga irin wannan mamaya musamman a nahiyar Turai, inda harshen manyan kasashe kan disashe kanana.

To sai dai masarautar Hausawa ta Turai da ke birnin Paris na Faransa, a cewar Sarkin tana shirya tarukan gargajiya da suka hada da bikin suna da na aure da wasannin kamar yadda aka sani a al’adar Bahaushe.

Yadda ake nadin Sarkin Hausawa a Faransa

Kasancewar mutum sarki a arewacin Najeriya da Nijar da ma sauran kasashen da Hausawa suke a fadin duniya na ta’allaka ne galibi da zamantowar mutum dan gado wato wanda za a nadin ya zama yana da sarautar a jininsa.

To sai dai kasancewar mutum Sarki a birnin Paris na Faransa da ke nahiyar Turai na samuwa ne ta hanyar kada kuri’a wato irin wadda ake kadawa a lokacin zabuka.

“An kada kuri’a ne aka zabe ni kuma ni ne mutum na farko da ya fara zama Sarkin Hausawan na Turai kuma har yanzu ni ne a kan karaga”, in ji Sarkin Hausawan Turai.

Wani karin banbanci tsakanin sarautar Hausa ta Turai da Najeriya da Nijar ita ce yadda makada da mabusa da maraya da kuma ‘yan tauri ke cashewa a yayin bukukuwan al’ada, a Turai hakan ba ya yiwuwa saboda rashin irin wadannan mutane.

“Insha Allahu a bana muna son mu dauko irin wadannan mutane daga Najeriya da Nijar domin halartar gagarumin bikin al’adar Hausawa da za mu yi a katafaren dandalin wasan al’adu na birnin Parisa.”

Girman masarautar Hausawa a Turai

Duk da cewa an kirkiri masarautar Hausawan Turan ne a birnin Paris na Faransa amma yanzu haka akwai rassan masarautar a kusan ilahirin kasashen Turai.

Sarkin Hausawan ya ce ” Masarautar na da cibiyarta ne a Paris amma tana da sassan a sauran biranen Turai inda suke da hakimai. Hausawan kasashen Turan ne dai ke zabar mutumin da suke ganin ya dace sai kuma a yi masa nadi a birnin Paris.”

Dangane kuma da yawan al’ummar Hausawa da masarautar Hausawan Turai ta san da zamansu, Sarki Jan Kado Labbo ya ce “kididdiga abu ne mai wuya amma muna da alkaluman da ke nuna cewa akwai Hausawa a Faransa kimanin 5000 sannan a Jamus akwai kiyasin dubu 10 inda kuma ake da mutum fiye da dubu 15 a Burtaniya. Akalla dai akwai Hausawa a Turai fiye da dubu 30.”

More from this stream

Recomended