Wani faifan bidiyo da ake yaɗawa a Najeriya wanda ke nuna yadda aka tayar da wasu Fulani makiyaya daga wani gari a jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin ƙasar na ci gaba da tayar da ƙura.
A cikin faifan bidiyon dai an jiyo muryar wani mutum ta na bayani cikin harshen Ingilishi, cewa an lalata wa Fulanin rugage da kayansu, ana kuma buƙatar su kwashe nasu-ya-nasu su tashi saboda ba a ƙaunar Fulani da Mi Yetti Allah a jihar.
Wasu dai na ganin akwai ƙanshin gaskiya a abin da bidiyon ya ƙunsa yayin da kuma wasu ke cewa akwai lauje cikin naɗi a lamarin.
BBC ta tuntuɓi ɗaya daga cikin Fulanin da aka tasa daga Ebonyi zuwa jihar Taraba ya ce tsoro da kuma hare-haren da ake kai masu ne suka tilasta musu yin ƙaurar.
A cewarsa, dalilin da ya sa suka tashi na da nasaba da kashe musu yaro da dabbobi da aka yi kuma ba tare da gwamnati ta yi wani abu a kai ba. duk da irin alƙawuran da take ɗaukar musu cewa hakan ba za ta sake faruwa ba.
Ya ce an sha yi musu barazanar za a ƙona gidajensu lamarin da ya sa hankalinsu da na iyalansu tashi, “matayenmu ba su da kwanciyar hankali”.
Sai dai ya musanta zargin da ake yi wa Fulani na aikata miyagun laifuka inda ya ce a baya, suna zaune da mutanen garin lafiya kafin fara kashe musu shanu.
Tuni dai rundunar ƴan sandan jihar ta Ebonyi ta ƙaryata batun cewa ana korar Fulani makiyayan daga jihar inda ta ce Fulanin sun tashi daga jihar Ebonyi ne don ra’ayin kansu.
Mai magana da yawun rundunar jihar DSP. Odah loveth obianuju ta ce sam al’ummar Fulani makiyaya ba sa cikin wani matsin lamba kuma makiyayan da suka fice daga Ebonyi zuwa Taraba sun yi haka ne bisa raɗin kansu.
Alhaji Bello Abdullahi Boɗejo, shugaban Mi Yetti Allah Kautal Hore na ƙasa, ya ce ba haka batun yake ba inda ya ce “ai bafulatani idan ya tashi tafiya ai ba zai rushe abin da ya gina ba”.
A cewarsa, ana nuna wa Fulani makiyaya fin ƙarfi sannan ya bayyana cewa akwai bayanai da suka bayyana irin abubuwan da ake yi wa Fulanin.