- Daga Harry Farley
- BBC News
Asalin hoton, Getty Images
Manyan malamai fiye da 370 daga sassan duniya daban-daban suna kira a haramta tiyatar sauya jinsi – inda ake mayar da mace namiji ko kuma namiji ya koma mace.
Malaman da suka yi wannan kira sun fito ne daga manyan addinan duniya da dama, kuma daga ciknisu fitattun masu goyon bayan auren jinsi daya ne.
Sun hada da Archbishop Desmond Tutu da kuma tsohon shugaban mabiya addinin Yahudu na Ireland David Rosen.
Sauran malaman addinin sun ce haramta tiyatar sauya jinsin ka iya kallon fasto-fasto a matsayin masu laifi.
Za a kaddamar da kiraye-kirayen haramta tiyatar sauya jinsi a wajen taron da ofishin harkokin ƙasashen waje da hula da kasashen rainon Ingila da ci gaba zai gudanar ranar Laraba.
Bishop na darikar Anglican da ke Liverpool, Paul Bayes, da Mary McAleese, tsohuwar shugabar Ireland, na cikin wadanda suka sanya hannu kan takardar neman haramta tiyatar sauya jinsin.
Firaiministan Birtaniya Boris Johnson ya jadda alkawarin da ya yi na haramta tiyatar sauya jinsi, inda a watan Yuli ya ce yin tiyatar “babban abin kyama ne” kuma “ba shi da mazauni a wannan kasar”.
Ya zuwa yanzu gwamnati ba ta wallafa cikakken bayani kan haramta tiyatar jinsin ba sai dai ta ce ta kaddamar da bincike kuma za ta fitar da tsarin “idan lokaci ya yi”.
Kasashe da dama sun haramta yin tiyatar, ciki har da Switzerland da wasu yankunan Australia da Canada da kuma Amurka.
Sharhi – daga Ben Hunte – Wakilin BBC kan auren jinsi
Tun daga shekarar 2018, firaiministoci biyu na Birtaniya sun yi alkawarin haramta tiyatar sauya jinsi amma har yanzu masu fafutuka na jira a dauki wannan mataki.
Daya daga cikin matsalolin haramta tiyatar ita ce yadda aka za a bayyana ma’anar “tiyatar sauya jinsi” da kuma yadda za ta shafi masu auren jinsi daya.
A yayin da alkaluman da gwamnati ta fitar suka nuna cewa an fi yi wa mata-maza tiyatar sauya jinsi a tsakanin dukkan masu auren jinsi, wasu masu fafutuka na fargabar cewa kowanne sauyi daga bangaren gwamnati zai iya yin watsi da tiyatar sauya jinsi bisa la’akari da asalin jinsin mutum da kuma mayar da hankali kan kasancewarsa mace ko namiji.
Wasu kuma na fargabar cewa sauyin zai iya wuce gona da iri.
‘Na shiga cikin mawuyacin hali‘
Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2018 kan mutane 108,000 mambobin kungiyar masu auren jinsi daya ta Birtaniya ya nuna cewa an taba yi wa kashi biyu daga cikinsu tiyatar sauya jinsi, sannan aka nemi yi wa kashi biyar tiyatar.
Manyan addinai, ciki har da Kiristanci da Musulunci da Yahudanci, suna tunatar da mabiyansu cewa duk wata mu’amalar jima’i da aka yi ta ba tsakannin mace da namiji ba, ba ta halasta ba.
Joe Hyman, mai shekara 28, ya tashi a matsayin Bayahude a arewacin London. Ya ce an nemi yi masa tiyatar sauya jinsi lokacin yana dan matashi.
Ya shaida wa BBC cewa “Ina so a yi mini tiyatar. Ba zan iya zama a matsayin dan luwadi ba kuma ni Bayahude ne. Ba na tsammanin iyayena za su yarda da hakan. Na shiga mawuyacin hali.”
Ya ce ya tattauna da masu yin tiyatar ta shafukan intanet da kuma a zahiri da zummar sauya jinsinsa.
“Hakan ya sa na tsani kaina, na zama wanda ya sauya jinsinsa, kuma a ko da yaushe ina cikin fargaba ina ganin abubuwan da nake yi ba daidai ba ne,” in ji shi.
Asalin hoton, Joe Hyman
Joe Hyman, wanda ka yi wa tiyatar sauya jinsi, ya ce hakan ya shafi lafiyar kwakwalwarsa
Malaman addinin sun yi kira a haramta duk wani nau’i na tiyatar sauya jinsi.
Sai dai wasu kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin addini daga bangaren addinai daban-daban sun ce haramta tiyatar zai yi karan-tsaye ga ‘yancin mutane na addini.